Jam’iyyar ta ce hukumar yan sandan sunyi kutse gidan dan takarar ta na kujerar dan Majalisar Wakilai ta Bauchi ta tsakiya Yakubu Shehu Abdullahi, wakilin Birni, inda suka karya kofar gidan da yake kiwon dawakai suka kama wasu mutanen da ke zaune a gidan ciki har da limamin masallacin gidan.
A hira da manema labarai da jam’iyyar PRP din ta gudanar a karkashin jagorancin shugaban reshen jam’iyyar na karamar hukumar Bauchi, Alhaji Suleiman Musa, ya bukaci babban sufeton yan sandan Najeriya da ya hana yan sandan jihar Bauchi cin zarafin yan jam’iyyar.
Shima anasa jawabin dan takarar kujerar dan Najalisar Wakilai na Bauchi ta tsakiya wakilin Birni, ya ce bayan ya kammala ziyarar kamfen sai ya sami labarin abin da yan sandan sukayi a gidan dawakansa.
A nasa ba’asin jami’in hulda da jama’a na hukumar yan sandan jihar Bauchi Kamal Datti, ya tabbatar da kama mutanen bisa zargin yunkurin tayar da hankali.
Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5