Tun da shugaban wanda ya dade akan mulki ya yi ikirarin lashe zaben da ake takaddama akai na tara ga watan Agusta, masu zanga-zanga suke fitowa tituna akai-akai suna neman da ya sauka kuma a saki fursunonin siyasa.
Lukashenko ya kafe akan shi ya lashe zaben da tazara mai yawa ta kashi tamanin cikin dari na kuri’un da aka kada, duk da zarge-zargen da ake ta yi a gida da wajen kasar na cewa an tafka magudi a zaben domin ya zarce kan mulki.
A karshen makon nan Belarus ta soke tantance ‘yan jaridar kasashen waje. A makon da ya gabata kuma kungiyar Tarayyar Turai wato EU, ta kakaba takunkumi akan jami’an Belarus kusan 40 da ake zargin su da sauya sakamakon zaben da kuma kame masu zanga-zanga.
Babu sunan Lukashenko a cikin jerin sunayen.
Fushin jama’a ya karu game da kamen na masu zanga-zanga inda aka kame fiye da mutane 7,500 da karuwar farmaki da ‘yan sanda suke kai musu.