Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsare Maria Kolesnikova Wata Jagoriya a Bangaren Adawar Kasar Belarus


Belarus Election
Belarus Election

Dambarwar siyasar kasar Belarus na dada kazancewa yayin da aka tsare jagoriyar siyasar kasar Belarus.

Jami’an kasar Belarus sun ce, a yau Talata an tsare Maria Kolesnikova, wata jagora a bangaren adawar kasar a lokacin da ta yi kokarin shiga kasar Ukraine.

Jami’an sun ce Kolesnikova na tafiya ne tare da wasu mambobin bangaren ‘yan adawa su biyu a lokacin da lamarin ya faru, Anton Rodnenkov da Ivan Kravtsov, wadanda dukansu biyu suka yi nasarar shiga Ukraine.

Ba a bayyana yadda tawagar ta su ta kai iyakar kasar ba.

Mataimakin Ministan harkokin cikin gida na Ukraine, Anton Gerashchenko ya bayyana a shafinsa na facebook cewa abinda ya faru a yau ba da son rai ba ne, illa kawai abin da ya kira kora ta karfi da yaji.

Wannan lamarin dai ya janyo kiraye kiraye daga kasar Jamus da Burtaniya inda suka umarci shugaba Alexander Lukashenko da ya bayyyana inda Kolesnikova ta ke, bayan da wasu maza, wadanda ba a san ko su waye ba, sanye da takunkumi a fuskokinsu, su ka yi awon gaba da ita.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG