Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Kin Jinin Shugaba Lukashenko Na Kara Zafi A Belarus


Masu zanga zanga a kasar Belarus
Masu zanga zanga a kasar Belarus

A kalla ‘yan kasar Belarus 100,000 ne suka mamaye titunan birnin kasar Minsk a jiya Lahadi, a wata zanga-zanga mafi girma ta kin jinin shugaba Alexander Lukashenko, bayan ya yi ikirarin samun nasara a zaben watan jiya da ake takaddama akai, da kuma abokan hamayyarsa suka ce yana cike da magudi.

'Yan Sanda sun ce sun kame masu zanga-zanga sama da 400 a birnin Minsk kuma suna ci gaba da kamen ya zuwa yammaci.

Yayin da jama’a ke ci gaba da nuna kin amincewarsu da Lukashenko, wanda ya yi mulkin kasar da ke karkashin renon Rasha na tsawon shekaru 26, Rashar ta ce za ta taimaka masa ta hanyar turo dakarunta a Belarus.

Masu zanga-zangar na da’awar cewa Sviatlana Tsikhanouskaya ce ta lashe zaben na 9 ga watan Agusta. Manyan jagororin adawa da dama an kullesu ko kuma sun arce daga kasar, inda a yanzu haka Tsikhanouskaya tana Lithuania.

Lukashenko ya musanta zargin cewa an yi magudi a zaben, kana yana zargin cewa wasu manyan kasashen waje ne ke hura wutar zanga-zangar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG