Yayin da gwamnatoci a nahiyar Turai ke takaddama a kan kakabawa kasar Bekarus takunkumi biyo bayan zaben watan da ya gabata, wasu tsofaffin ‘yan diflomaisya da masu sharhi sun yi kira ga wadannan kasashe cewa kada su auna shugaba Alexander Lukashenko da manyan jami’an gwamnatinsa kadai, har ma da kawayenta na Rasha.
Takaita takunkumin ga wasu jama’a kadai zai shafin tasirin takunkumin, inji Anders Aslund, wani tsohon dan diflomasiyar kasar Sweden.
Yace babbar manufa itace duk wani takunkumi kada ya zama jan kunne ga wadanda suke da hannu a rikicin zabe na ranar tara ga watan Agusta kadai ba, amma ya zama izina ga ‘yan kasar Belarus da ‘yan kasar Rasha dake taimakawa gwamnatin Lukashenko a kan kungiyoyin
Shima shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fada a shekararnjiya Lahadi cewa shugaban na Belarus ya sauka da mulki.
Facebook Forum