"Yan Sanda Sun Kama Kudin Jabu na Miliyoyin Nairori

Rudunar ‘Yan Sandan jihar Borno, ta nuna mutane goma sha biyu, da ta kama da ake zargi da laifufuka da suka hada da fashi da makami da kuma buga kudin jabu ga manema labaru a garin Maiduguri, da kuma wani dan shekaru ashirin da daya da haihuwa da ya yiwa wata yarinya ‘yar shekaru goma sha biyu fyade.

Wani maisuna Adam Ajit, da aka kama da kudin jabu har Naira miliyan 4 da dubu 500, yace shi attajiri ne amma harkar ‘yan Boko Haram ne ya jefa shi cikin wannan mummunar harka ta kudin jabu.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar ta Borno Mr.Aderemi Opadokun,da ya nuna mutane yace suna ci gaba da gudanar da bincike akan wadannan mutane da aka kama kuma nan bada jimawaba za’a gurfanar dasu a gaban kotu.

Kwamishinan ‘yan Sandan yace an kame mutanen da ake zargi da fashi da makami su biyar a karamar hukumar Kwaya Kusar dake jihar Borno, da Bindigogi.