Yan sandan a Hong kong sun yi amfani da barkwnon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan tsarin dimokaradiyya, wadanda su ka ci zarafin wani babban jami'in gwamnatin China, yayin da ya yi yinkurin bayyana dalilin China, na sa tsarin zabar 'yan takarar Shugabancin yankin karkashin kulawarta sosai.
Yayin da Mataimakin Shugaban Kwamitin dindindin na China National People's Congress Li Fei, ya fara jawabi ma 'yan majalisar dokokin Hong Hong a yau Litini, sai wasu 'yan majalisar da masu zanga-zangar da duk ke goyon bayan tsarin dimokaradiyya su ka masa ihu.
"Gwamnatin China na so ne ta tilasta ma Hong Kong irin abin da ta yi mata alkawarinsa, wato kasa daya tsare-tsare biyu. I na ganin ai abin da aka yadda da shi a kasa da kasa shi ne, bai kamata a ce da lallai ko tilas dangane da 'yan takarar duk wani zabe ba.
Li ya cigaba da jawabinsa bayan da 'yan sanda su ka fatattaki masu zanga-zanga daga waurin.
"Dukkanninmu mun san cewa mamaye wurin laifi ne. Tarihi daga kasashen waje ya nuna sau da dama, kuma tarihin ita kanta China ya nuna cewa muddun mu ka bi ra'ayin haramtattun kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da wasu mutane ke izawa, hakan zai dada haifar da karin haramtattun kungiyoyin ne sosai. Saboda haka, lokacin da Kwamitin Dindindin na jam'iyyar National People' Congress ya yanke wannan shawara ta shi, sai da ya yi nazarin al'amarin sosai, kuma da zummar kare doka da oda da kuma tabbatar da kwanciyar hankali mai dorewa a Hong Kong, don ta iya tsara manufofinta sosai"