Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Samar ma Miliyoyin 'Yan Syria Abinci


Ban Ki-moon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Ban Ki-moon Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta samar ma miliyoyin 'yan Syria dake karkashin 'yan tawaye abinci domin kubutar dasu daga azabar yunwa.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice tace ta raba tallafin abinci ga mutane miliyan hudu d a dubu dari daya a Syria cikin watan Agustan nan da ya shige, sakamakon budi da ta samu na shiga kasar sosai.

Nasarar da hukumar ta samu wajen raba abincin ya biyo bayan kudurin da MDD ta zartas data baiwa hukumar samar da abincin ikon shiga sassan kasar dake hanun ‘yan tawaye ba tareda izinin gwamnatin kasar ba.

Tunda farko a jiya talata, kwamandan sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD daga kasar Fiji Birgediya janar Moses Tikoitoga, yace kungiyar mayakan sakai mai alaka da al-Qaida ta gindiya sharudda da take bukata a cika kamin ta saki sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD su 45 da suke garkuwa da su tun ranar talata da suka sace su a tuddan Golan.

Janar Moses yace kungiyar ‘yan tawayen da ake kira Nusra sun nemi da a janye sunan kungiyar daga jerin kungiyoyi da aka ayyana su a matsayin na ta’addanci, a tura kayan agaji ga sassa da suke kusa da birnin Damascuss, sannan a biyasu diyyar kashe ‘ya’yan kungiyar uku da aka kashe a fada.

Babban sakataren MDD Ban ki-moon yayi kira da a sake su, ranar litinin magatakardan MDD yace hukumomin majalisar suna shawarwari da kungiyar da nufin ta saki sojojin da take garkuwa dasu.

XS
SM
MD
LG