Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kungiyar Daular Islama sun ja Baya a Iraki


Dakarun Iraki rike da tutar 'yan kungiyar Islama.
Dakarun Iraki rike da tutar 'yan kungiyar Islama.

Jami'ai a Iraki sun ce sojojin Irakin, da dakarun Kurdawa da kuma mayakan 'yan Shi'a, sun danna cikin garin Sulaiman Bek.

Jami'ai a Iraki sun ce sojojin Irakin, da dakarun Kurdawa da kuma mayakan 'yan Shi'a, sun danna cikin garin Sulaiman Bek, kudu da Kirkuk a yau dinnan Litini, wanda ya kawo karshen killace shi na tsawon watanni uku da mayakan Daular Islama su ka yi.

Sojojin na Iraki sun kutsa cikin garin ne kwana guda bayan da su ka wargaza kawanyar tsawon watanni biyu da 'yan Daular ta Islama su ka yi ma garin Amirli da ke kusa.

Tuni aka yi ta shiga da kayan agaji a garin, ciki har da kayan abinci da ruwa da Amurka ta yi ta jehowa daga jiragen sama.

Sojojin Amurka sun fadi yau Litini cewa sun cigaba da kai hare-haren jiragen sama kan wuraren 'yan Daular Islama, wato sau uku kenan su ke kai hare-hare daura da madatsar ruwan Mosul tun daga ranar Lahadi.

A yau Litini din har ila yau, Firayim Ministan Burtaniya David Cameron ya gaya ma Majalisar Dokokin kasar cewa Burtaniya na goyon bayan hare-haren jiragen saman da Amurka ke kaiwa kan ISIL a Iraki. Ya kara da cewa Burtaniya na bukatar karin sabbin dokokin yaki da ta'addanci don fuskantar barazanar da 'yan Daular Islama ke yi da kuma 'yan Burtaniyar da ke yaki ma kungiyar.

XS
SM
MD
LG