Amurka zata taimakawa Najeriya da makwabtanta su tunkari Boko Haram ta wajen kaddamar da wani matakin tsaro kan iyakokinsu nan bada jumawa ba.
Mukaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da shiyyar Afirka Linda Thomas Greenfield ce ta bayyana haka jiya Alhamis lokacinda take magana da jami’an gwamnatin Najeriya a Abuja a dai dai lokacinda kafofin yada labaran kasar suke cewa ‘yan kungiyar Boko Haram din sun kama garin Bama.
Da take bada karin haske kan wannan batu wata kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Marie Harf tace shirin yana karkashin wani asusu da shugaba Obama ya bada sanarwa akai a lokacinda aka yi taron koli da shugabannin Afirka
Marie Harf tace shirin zai hada da Najeriya da makwabtanta Cadi, da kmaru d a Nijar, kuma ta gayawa taron cewa a shirye Amurka take ta taimakawa Najeriya ta tunkari barazanar Boko Haram, daga nan tayi kira ga mahakuntan Najeriya cewa su bullo da shiri sahihi na kare al’umarsu.