‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kulle kokofin shiga Majalisar Dokoki, biyo bayan wata wasikar da kakakin Majalisar ya aikawa ‘yan Majalisar cewa an dage zaman Majalisar saboda da wani aiki daya taso a Abuja.

Rashin jituwa ya bayyana tsakanin yawancin ‘yan Majalisar Dokokin jihar Bauchi da kuma bangaren gwamnatin jiha, inda ‘yan Majalisun ke zargin gwamna da mulkin kama karya biyo bayan gudanar da zaben fidda ‘yan takara da bai samu amincewar yawancin yan takarar ba.

Tura jami’an tsaron zuwa Majalisar Dokokin da kuma gidan dan Majalisa Yakubu Abdullahi, wanda ake kira Yakubu wowo na da nasaba da siyasa da kuma batun yiwuwar tsige kakakin Majalisar Kawuwa Shehu Damina, saidai hukumar ‘yan sandan tabakin kakakinta DSP Kamal Datti, inganta tsaro ne akeyi a Majalisar dama gidan dan Majalisar.

DSP Kamal Datti, ya ce basu rufe kofofin Majalisar ba, sun dai dauki matakin kara tsaro ne kasancewar shigowar kakar zabe, akwai yiwuwar wasu bata gari su iya amfani da wannan dama su tada hankali a wurare masu muhimmanci.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar Dokokin Jihar Bauchi - 3'20"