Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Jihar Kano Zata Bincike Batun Bidiyon Ganduje


Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano
Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Majalisar dokoki ta jihar Kano tace gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da dan kwangilar da ake zargin ya bashi toshiyar baki da kuma mawallafin Jaridar data buga batun zasu gurfana a gaban kwamitin data kafa domin bincikar lamarin

Bayan tafka mahawara akan batun a zaman ta na jiya litinin, majalisar ta kafa kwamitin mai wakilai 7 domin gudanar da binciken.

Hon Labaran Abdul Madari wanda shine ya gabatar da kudiri kan batun ya bayyana cewa majalisa ta dauki wannan matakin ne domin a kan kundin tsarin mulki take tafiya, kuma kundin tsarin mulkin ya bukacesu, su gudanar da bincike domin tantance gaskiyar Magana, yadda zasu sanar da al’ummar da suke wakilta.

Yace yadda aka sami ci gaba a fannin hanyoyin sadarwa a Najeriya, yana iya yiwuwa a harhada hoto ya zama tamkar haka lamarin yake, sabili da haka gudanar da bincike zai taimaka wajen tantance gaskiyar lamarin.

Aikin kwamitin ya hada da samun cikakken bayani daga wadanda suka buga labarin da kuma neman kwararru a fannin tantance sahihancin labarai da hotuna da aka yayatawa a shafukan yanar gizo.

Dan majalisa Labaran Abdul Madari ya yi wannan bayanin ne a hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari.

Saurari cikakkar hirar:

Majalisar Dokokin Kano Ta kafa kwamitin Bincike-3:31"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG