Ana zargin mutanen da aka kama ne da hannu a ayyukan ta’addanci da suka hada da kisan jama’a da satar shanu da kuma garkuwa da mutane a jahar Neja.
Cikin watan da ya gabata ‘yan sandan sun kama kimanin mutane 200 da ake zargin suna da hannu a ire-iren wadannan laifuffuka a jahar. A wani taron manema labarai a Minna, kakakin ‘yan sandan jahar Neja DSP Bala Elkana, yace sun sami nasarar kwato makamai daga hannun mutanen da aka kama.
Haka kuma yace sun kwato wasu bindigogi 12 da aka shigo da su daga jamhuriyar Benin, sai kuma wasu kananan bindigogi da aka sarrafasu a Najerya. Sai kuma shanu da aka kwato daga hannun barayi har 672.
Kungiyar Fulani ta Miyatti Allah, ta ce ta gamsu da kokarin jami’an tsaron na kokarin kawar da bata gari a tsakanin al’umma. Alhaji Bello Badejo, yace suna nan suna kokarin wayar da kan matasan Fulani kan muhimmancin rike al’adunsu na kwarai da suka gada tun daga iyaye da kakanni.
Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5