Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Gombe PDP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Jahar


PDP
PDP

Jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe zaben dukkannin yankunan kananan hukumomin jahar Gombe.

A cewar kwamishinan hulda da jama’a na hukumar zabe a jahar Gombe, Kala Kal Kudi Lubo, yace an gama zabe cikin kwanciyar hankali inda kuma sakamakon zabe ya nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta samu nasarar lashe zaben kujerun kananan hukumomin jahar 11 baki ‘daya.

Sai dai kuma gamaiyar jam’iyyun adawa a taron manema labarai sunyi watsi da sakamakon zaben.

Kakakin gamayyar jam’iyyun siyasa a jahar Gombe, wanda kuma shine shugaban riko na jam’iyyar APC, Alhaji Idris Barde Gubana, yace baki ‘dayansu ‘yan jam’iyyun adawa na jahar Gombe, basu gamsu da zaben jahar ba. kuma zasu dauki matakin shigar da ‘kara kotu.

A yau dai ake sa ran gwamnan jahar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dan Kwambo, zai rantsar da sabbin shugabannin ‘kananan hukumomin da aka ce sun lashe zaben domin fara aiki.

Domin karin bayani ga rahotan Abdulwahab Mohammad daga Gombe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG