Long Goemai Martins Sheldas yayi alkawarin hada kan al'umma da bunkasa aikin noma da wanzar da zaman lafiya.
Masarautar Long Goemai dai masarauta ce mai dadadden tarihi wanda bincike ya nuna cewa an kafata tun cikin karni na goma sha takwas wanda yanzu shi sabon Long Goemai din shi ne sarki na talatin da daya.
Long Goemai Miskom Martins Sheldas ya fara ne da nuna farin cikinsa bisa ga wannan nasara da Allah Ya bashi. Yace "sarauta dai kowa ya samu dole ya ji dadi kuma abun farin ciki ne gareni da 'yauwana da iyalina duka." Sarkin ya cigaba da cewa su Goemai sarautarsu ce ta manoma. Sarki shi ne uban hatsi, inji sarkin. Yace idan an samu Long Goemai za'a samu bunkasa a harkokin noma, abinci zai kuma wadata a garin.
Sai dai abu mafi mahimmanci, inji sarkin shi ne zaman lafiya. Idan gari ya zauna lafiya to yana da sarki mai imani. Sarki mai imani baya nuna banbancin kabilanci ko addini saboda duk an zama daya.
Long Goemai Martins Sheldas ya kira al'umma su lura da kiyaye zaman lafiya domin shi ne zai biya masu bukata.
Dubban jama'a ne daga sassan Najeriya daban daban suka hallara a garin Shendam domin taya sabon sarkin murnar nadinsa.
Wasu 'yan kabilar Goemai sun bayyana abun da suke bukata daga sarkin nasu. Kusan dukansu suna fatan ganin a zauna lafiya a masarautar.
Wadanda suka yi magana a kan sabon sarkin sun ce yanada saukin kai kuma baya nuna banbanci. Idan ya cigaba da hakan zai ji dadin sarautar.
Ko gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura wanda ya kasance a wurin nadin tare da sarakunan gargajiya na jihar Nasarawa yayi shaida mai. kyau akan sarkin. Yace mutanen Plateau da Shendam sun yi sa'ar samunsa a matsayin sarki.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum