'Yan sanda A Ingila Sun Kama Mutane 4 Kan Satar Sauraron Zantuttuka a Waya

'Yansanda da sojojin kundunbalan Ingila suke atisai na matakan tsaro domin wasanin motsa jiki na Olympics mai zuwa.

‘Yan Sandan Ingila sun kama mutane hudu cikinsu harda dan sanda daya, a abin fallasa nan na satar sauraron zantuttukan mutane a waya da ake zargin jaridar News of the World.

‘Yan Sandan Ingila sun kama mutane hudu cikinsu harda dan sanda daya, a abin fallasa nan na satar sauraron zantuttukan mutane a waya, da ake zargin tsohuwar jaridar News of the World, da ta shahara wajen wallafa gulmace-gulmace a Ingila.

Rundunar ‘Yansandan tace an kama mutane uku da safiyar Asabar din nan a gidajensu dake cikin birnin Landan, ko kuma a kewayen birnin.

Jami’in ‘Yan sandan kuma an kamashi bayan ya iso bakin aiki a safiyar yau Asabar.

Mutanen hudu da aka kama shekarunsu na haifuwa ya kama daga 29-56, sun shiga hannu ne kan zargin cin hanci da rashawa. Ba a gurfanar da su a gaban kotu ba tukuna.

‘Yansanda suka ce bayanan da kamfanin tsohuwar jaridar ya bayar su suka taimaka aka kai ga kama mutanen.