Ana kyautata cewa takarar neman shugabancin kungiyar kasashen Afirka ce za ta fi daukan hankula a wajen taron kolin kungiyar da za a fara yi a yau Lahadi a Addis Ababa babban birnin kasar Ethiopia.
A jiya Asabar kungiyar kasashen Afirkar ta yi bikin kaddamar da sabon ginin cibiyar ta, ko helkwatar ta a birnin Addis Ababa, wadda kasar China ta gina da kudin ta dola miliyan 200 kuma ta ba ta kyauta. Babban mai ba gwamnatin kasar China shawara a kan al’amuran siyasa, Jia Qinglin, shi ne ya bude sabon ginin a yayin wani bikin da ya samu halartar frayim ministan kasar Ethiopia, Meles Zenawi da wasu shugabannin kasashen Afirka da kuma jakadun wasu kasashen waje.
Jia ya ce Cibiyar wadda aka gina a gurbin wani tsohon gidan kaso mai tsananin tsaro, shaida ce da ke tabbatar da abutta ko abokantakar da ke tsakanin kasar China da al’ummar Afirka. Haka kuma ya yabawa yadda kasuwanci ke dada bunkasa tsakanin China da kasashen Afirka, ya ce China ce abokiyar huldar kasuwancin Afirka mafi girma, kuma gwamnatin kasar China ta zuba jarin da ya kai dola miliyan dubu 13 a nahiyar Afirka.
Frayim Ministan Ethiopia Meles Zenawi ya yabawa abun da ya kira farfadowar Afirka, wadda ta samu bisa yin koyi da tsarin tattalin arzikin gwamnatin kasar China. Haka kuma frayim ministan na kasar Ethiopia ya yi amfani da damar da ya samu, ya soki lamirin tsarin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya na wannan karni, wanda ya kwatanta da neman kibar, da ta tono rama.