Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mai kula da harkokin Afirka, Johnnie Carson zai jagoranci tawagar harkokin makamashi zuwa kasashen Mozambique da Tanzaniya, da Kenya, da Nijeriya da Ghana daga ran 6 ga watan nan na Fabrairu zuwa 17 ga watan.
Wannan tawagar ta manyan jami’an gwamnatin Amurka da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu za su gana da manyan jami’an gwamnatocin kasashen da za su ziyarta don su tattauna kan kalubalen da ke akwai wajen saka jarin Amurka a harkokin samar da makamashi.
Wakilai daga bangaren ‘yan kasuwan Amurka za su wakilci kamfanoni don kafa gagarimin tubulin ayyukan samar da makamashi.
Wannan hanzarin zai jaddada matsayin kafa ginshikin tattalin arziki wajen samun cigaba mai dorewa da kwanciyar hankali ya kuma nuna hobbasar Amurka a yankunan.
Amurka dai ta himmantu ga taimakawa da kuma saukaka harkokin kasuwanci da saka jari ta wajen shirye-shiryenta da cibiyoyin fadakarwa a nan Amurka da kuma ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje, a cewar bayanin.