Yan gwaggwarmayar kasar Siriya sun ce dakarun gwamnati sun kai samame a wani gari dake babban birnin kasar inda masu tarzoma suke taruwa a zanga zangar watanni goma da ake yi ta kin jinin shugaba Bashar al-Assad.
Kungiyar mai kula da harkokin kare hakin bil’adama a Siriya dake da zama a birnin London tace dakaru da dama sun shiga garin Douma yau alhamis da safe. Bisa ga cewar kungiyar, bijirarrun sojoji sun kwace ikon garin ranar asabar.
A halin da ake ciki kuma kungiyar hadin kan larabawa ta ce, janye masu sa ido da kasashen yankin Gulf suka yi, ba zai hanata gudanar da aikinta a Siriya ba.
Wani jami’in kungiyar ya bayyana jiya Laraba cewa, masu sa ido ‘yan kasar Mauritaniya goma sha biyar da Palasdinawa goma da kuma Misirawa shida zasu tafi Siriya cikin mako guda mai zuwa. Zasu maye gurbin masu sa ido daga majalisar kasashen yankin Gulf wadanda gwamnatocinsu suka hakikanta cewa za a ci gaba da zubar da jinni da kuma kashe farin kaya da basu ci ba basu sha ba a Siriya.
Kasashen larabawa dake yankin Gulf suna kara nuna goyon bayan daukar matakin kasa da kasa a kan Siriya cikin makonnin da suka shige, yayinda dakarun dake goyon bayan Assad suke ci gaba da kai hari kan masu zanga zangar lumana suna kuma suke kazamin fada da sojojin da suka bijire.