Sai dai suna masu jan hankulan shugabanin kasashen yankin su zuba ido don tilasta wa gwamnatin ta Mali yin biyayya ga sharudan da aka gindaya mata.
Gamsuwa da yadda gwamnatin rikon kwaryar Mali ta nuna alamun shirya zaben da zai mayar da mulki a hannun fararen hula cikin watanni 24 a maimakon shekaru 3 da ta ayyana a can farko ya sa kungiyar CEDEAO dage takunkumin da ta kakaba wa kasar sakamakon juyin mulkin watan Agustan 2020 da wanda ya biyo baya a watan mayun 2021.
A ra’ayin shugaban kungiyar Voix des Sans Voix Nassirou Saidou wannan mataki zai fitar da talakkawa daga kangin da suke ciki yau shekaru sama da 2.
Shugaban kungiyar matasa ta MOJEN Siraji Issa na ganin matakin a matsayin wani abinda zai samar da canjin tunani a wajen ‘yan Mali.
A ra’ayin wani dan jarida Souley Maje Rogeto mamba a kungiyar RJPSC can dama kungiyar ta kasashen yammacin Afrika dokin zuciya ne ta hau a wani lokacin da ‘yan Mali ke neman mafitar matsalolin da suka dabaibaye kasar wadanda suka hada da matsalar tsaro da rigingimun siyasa.
A bisa la’akari da take taken mukarraban gwamnatin rikon kwayar ta Mali kungiyar CEDEAO ta gindaya sharuda ciki har da batun hana wadanan jami’ai shiga zabubukan da za a gudanar a nan gaba.
Tun a tsakiyar watan da ya gabata ne masu nazari akan al’amuran yau da kullum suka gargadi shugabanin kasashen yammacin Afrika su dubi halin kuncin da talakawan Mali suka shiga sakamakon takunkumin da suka kakabawa kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5