Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ECOWAS Ta Hana Najeriya Hukunta Wadanda Suke Amfani Da Twitter


Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO a Ghana (Facebook/ECOWAS/CEDEAO)
Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO a Ghana (Facebook/ECOWAS/CEDEAO)

Matakin da kotun ta dauka na zuwa ne, sa'o'i bayan da shugaban Najeriya ya amince da samar da wata tawaga da za ta yi zaman sasantawa da Twitter.

Kotun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta ce hukumomin Najeriya su dakatar da duk wani yunkuri na hukunta wadanda suke amfani da Tiwtter a kasar.

Kotun har ila yau, ta yanke hukuncin cewa kada hukumomin kasar su ce za su kama, ko hukunta Twitter, ko wani kamfani da ke samar da hanyoyin kai wa ga kafafen sada zumunta, ko gidan rediyo ko talabijin.

Alkalan kotun sun dauki wannan matsaya ce, kafin a kammala sauraren shari’ar.

Tun bayan haramcin da Najeriya ta saka akan Twitter, wasu 'yan kasar kan yi amfanin da kafar VPN ta gashin-kai wajen shiga shafin, abin da hukumomin kasar shi ma suka haramta tare da yin barazanar hukunta duk wanda aka kama yanayin hakan.

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da adalci a Najeriya ce ta shigar da hukumomin kasar kara a gaban kotun ta ECOWAS.

Kafafen yada labaran kasar da dama sun ruwaito cewa, kotun ta dauki wannan mataki ne bayan da ta kammala sauraren lauyoyin SERAP Femi Fala da lauyan gwamnati Maimuna Shiru.

An dage ci gaba da sauraren karar zuwa 6 ga watan Yulin 2021 kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook, SERAP ta ce ta nemi kotun da “ta dakatar da gwamnatin Najeriya da Ministan yada labarai Mr. Lai Mohammed daga umarnin da suka bayar wanda ya sabawa doka, inda suka ba kafafen talabjin da na rediyo umarnin su goge shafinsu na Twitter.”

A farkon watan Yuni Najeriya ta haramta amfani da shafin na Twitter.

Haramcin na zuwa ne bayan da kamfanin ya goge wani sakon da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya wallafa wanda ya yi gargadi ga masu ta da kayar baya a kudu maso gabashin Najeriya, sakon da Twitter ya ce ya saba ka’idojinsa.

XS
SM
MD
LG