Wani rahoto da cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa, sama da mutane miliyan 2 ne aka yi garkuwa da su daga watan Mayun 2023 zuwa watan Afrilun 2024.
WASHINGTON DC —
Rahoton yace ‘yan Najeriya sun biya kudin fansa har dala biliyan 1.42 ga masu garkuwa da mutane a cikin shekara guda.
Sannan fiye da mutane 600,000 ne aka kashe, yayin da aka yi garkuwa da sama da miliyan biyu a fadin kasar daga watan Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
Rahoton yace ‘yan ta’adda masu dauke da makamai, da aka fi sani da ‘yan bindiga, suna haddasa tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Rahoton ya ce kaso 91% na garkuwa da mutanen na neman kudin fansa ne, yayin da kaso 2.4% ya danganci manufofin siyasa, ta’addanci ko sauran mugayen laifuffuka.
Rahoton yace ‘yan Najeriya sun kashe dala biliyan 1.4 domin kubutar da ‘yan uwansu daga hannun masu garkuwa da mutane.