Wata majiyar ‘yan jarida da wakilin sashen Hausa Sule Mumuni Barma ya tuntuba ta wayar tarho ta bayyana cewa dimibin jama’a a karkashin jagorancin kungiyoyin fararen hula ne suka fito kan titunan birnin Tilabery a yau Alhamis da safe domin nuna rashin amicewarsu da tsarin kasafin kudin shekarar dake shirin kamawa, saboda yadda suke masa kallon mai kunshe da wasu sabbin haraji da ka iya jefa talakawa cikin halin kuncin rayuwa.
A birnin zinder kuwa daruruwan mutane ne suka yi cincirindo dazu da hantsi don zuwa fadar gwamnan jiha inda suka damka masa takardar nuna adawa da wannan tsarin kasafin.
Sabanin yadda abin ya wakana a wadannan biranen, a Yamai hukumomi sun haramta gudanar da wannan jerin gwanon na ranar 21 ga watan Disamba, mafari kenan da kungiyoyin kare hakkin jama’a suka dage zuwa jibi Asabar amma kuma suka bukaci mazaunan birnin Yamai suyi yajin aiki na gama gari a tsawon wunin yau Alhamis.
Sai dai a zagayen da muka gudanar a manyan titunan birnin, mun lura cewa wasu mutane sun bude shaguna yayinda wasu shagunan da dama ke rufe sannan cinkoson motocin haya ya ja da baya sosai abinda ke nufin kiran ya karbu rabi da rabi.
Ko ya kungiyoyin fafutikar da suka bukaci mazaunan Yamai su kauracewa harkoki a yau ke kallon wannan al’amri? Nasser Sa’idu na kungiyar MPCR ya ce, ko dayake ba duka mutane suka yi abinda suke so ba, yayi imani mutane dayawa sun amsa wannan kiran.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa Ibrahim Garba na ganin rashin isarda sako zuwa ga ‘yan kasuwa akan lokaci ne ya janyo wannan koma bayan gwagwarmayar.
Wakilin na sashen ya kuma tuntubi kakakin gwamnatin Nijar Assoumana Malan Issa ta waya don jin matsayin gwamnati amma bai daga wayar ba.
Kungiyoyin dake Allah wadai da sabuwar dokar harajin na Nijar sun bayyana shirin fitowa akan titunan Yamai a ranar Asabar 23 ga watan da muke ciki.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5