Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Ba Fannin Tsaro Kaso Mafi Tsoka a Kasafin 2018


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Niger
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Niger

A jawabin bikin cika shekaru 59 da kasarsa ta samu 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na kasar Faransa, shugaba Mahamadou Issoufou ya bayyana dalilin ba fannin tsaro kaso babba a kasafin kudin badi.

A jawabinsa na tsawon mintuna 15 da ya yi wa kasar, Shugaba Mahamadou Issoufou ya fayyace dalilan gwamnati na kebe babban kaso a tsarin kasasfin kudin kasar na 2018.

Ya yi hakan ne, a cewar shi, domin horas da jami'an tsaro tare da samar da bayanan sirri da kayan aiki na amfanin cikin gida da kuma wadanda suke taimakawa kasar ta fannin soji.

Kasashen yankin tafkin Chadi da suka hada da Najeriya da Chadi da Kamaru na da wata rundunar hadin gwiwa da ke yaki da kungiyar Boko Haram.

A wani gefen kuma kasar za ta taimaka wa sabuwar rundunar tsaro ta yankin Sahel mai kunshe da askarawan Mali, Burkina Faso da Mauritania wadda take da alhakin murkushe 'yan ta'addan arewacin Mali.

Ga rahoton Sule Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG