Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waye Zai Lashe Zaben Jam'iyar ANC a Afirka ta Kudu?


Nkosazana Dlamini-Zuma (Hagu) tana zance da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa (Dama) gabanin zaben jam'iyar ANC mai mulki
Nkosazana Dlamini-Zuma (Hagu) tana zance da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa (Dama) gabanin zaben jam'iyar ANC mai mulki

Masana na hasashen cewa akalar siyasar Afirka ta kudu na dab da sauyawa yayin da dubban wakilan jam'iyar African National Congress ANC mai mulki, ke shirin zaben sabon shugaban jam'iyar.

Dubban wakilai na shirin kada kuri’a a yau Lahadi domin zaben sabon shugaban jam’iya mai mulki ta ANC a Afirka ta Kudu.

Wannan zabe ana mai kallon mai muhimmanci lura da yadda ake tunanin zai iya sauya akalar siyasar kasar, wacce ta yi fama da mulkin wariya a shekarun baya.

Kusan mambobin jam’iyar ta ANC 5,000 ne ke shirin kada kuri’a a zaben da za a yi a Johannesburg, domin neman sabon shugaban jam’iyar da zai gaji Jacob Zuma, shugaban kasar mai ci.

Zuma zai sauka a mukamin shugaban jam’iyar ne yayin da ake zarginsa da badakalar cin hanci.

Amma dai zai ci gaba da rike mukaminsa na shugaban kasa kafin a yi zabe a shekarar 2019.

Fitattun mutane biyu ne ke takarar kujerar shugabancin jam’iyar da suka hada da mataimakin shugaban kasa Cyril Ramaphosa da kuma Nkosazana Dlamini Zuma.

Dlamini Zuma wacce ta taba auren shugaba Zuma har na tsawon shekaru 16 ta kasance mai fada a ji a jam’iyar ta ANC.

Tana kuma da kwarewa a fannin harkokin diplomasiyya.

Sai dai ana ganin mai yiwuwa wasu ‘yan takarar su sake bayyana kafin a gudanar da zaben.

Tun bayan da aka maido da tsarin mulkin dimukradiya a shekarar 1994, jam’iyar African National Congress ke lashe kusan dukkanin zabukan da aka yi.

Ana kuma ganin wanda ya lashe zaben shugabancin jam’iyar, shi zai iya zama dan tankarar jam’iyar a zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2019.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG