Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Dake Rikici a Sudan Ta Kudu Sun Hadu Don Sasantawa


Mambobin bangarorin da ke rikici a Sudan ta Kudu sun hadu a wani taro da ake gudanar wanda ake fatan za a samar da yajejeniyar tsagaita wuta zuwa ranar Juma’a.

Sama da mambobi 100 ne daga kungiyoyi da dama suke ganawa a taron da hukumar IGAD ta shirya a Addis Ababa, da zummar farfado da yajejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 2015.

Wakilan kungiyoyin dake fada da makamai da ma wanda basu da makamai sun hadu jiya Talata, a hedikwatar kungiyar tarayyar Afirka dake birnin Addis Ababa don tattauna samar da dawwamammiyar yajejeniyar zaman lafiya da ake sa ran za a cimma kan ranar Juma’a, idan Allah ya kaimu.

Kungiyoyin wanzar da zaman lafiya a taron sun nemi kungiyoyin dake fada da juna da su fara ajiye makamansu, yayin da ake gudanar da tattaunawar. An dai bayar da rahotan ci gaba da fada tsakanin dakarun gwamnati da na ‘yan aware masu goyon bayan Riek Macharin Lasu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG