YAOUNDÉ, CAMEROON, ‘Yan Nijar mazauna Kamaru sun haɗu ƙwansu da ƙwarƙwata, sun fito daga dukkan kusurwoyin kasar domin shiga zaben. Masu fafutuka na jam'iyyun siyasa daban-daban sun gudanar da taruka a gundumar Nkomkana da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru.
Da farko dai mun halarci taron magoya bayan jam'iyyar PNDS TARAYYA mai mulki Inda aka gudanar da jawabai da kiraye-kirayen karfafa jam'iyyar shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum albarkacin zaben ‘yan majalisa na bangare.
Alhaji Sahabi Jihadi, daya daga cikin jagororin taron ya bayyana farin cikin sa kan yadda ‘yan ja'miyar suka amsa kira.
Shugabar matan PNDS Tarayya a Yaounde Hadjiya Kadi ita ma ta tofa albarkacin bakin ta musamman kan gudun mawar matan jam'iyar PNDS.
Haka kuma a bangaren jam'iyyar adawa ta MODEN FA LUMANA, ita ma ta hada taro a wannan rana.
A ranar 18 ga watan Yuni ne aka shirya gudanar da zaben.
Kasar ta Nijar na daya daga cikin kasashen Afirka da suka bai wa 'yan Kasar mazauna waje damar zabe a ƙasashen zaman su, sabanin wasu kasashen Afirka kamar Najeriya da Kamaru.
Saurari cikakken rahoto daga Mohamed Bachir Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5