'Yan Najeriya Suna Zaben gwamna Da Wakilan Majalisar Dokoki.

'Yan Najeriya suke layi domin zaben Gwamna.

‘Yan Najeriya suna zaben gwamnoni,kashi na uku a zaben kasa baki daya,da tuni ya janyo tashen tashen hankula.

Sokoto Kebbi Elections

Taraba Elections

‘Yan Najeriya suna zaben gwamnoni,kashi na uku a zaben kasa baki daya,da tuni ya janyo tashen tashen hankula.

A yau Talata bama-bamai uku sun tashi a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar,kwana biyu bayan wasu fashe fashe a birnin da ya halaka mutane uku ya jikkata wasu 14.

An sami rahotanni da ke cewa an bude dukkan rumfunan zabe,sai dai akwai daruruwan matasa masu yi wa kasa hidima da suka ki zuwa bakin aiki a arewacin Najeriya inda galibi aka sami tashe tashen hankula.

Jaridun Najeriya sun bada labarin cewa jihohi dake kudancin Najeriya suna kwashe ‘yan jihohinsu dake aikin bautar kasa.

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama tace an kashe mutane akalla 500 a tarzomar da ta biyo bayan bayyana sakamkon zaben shugaban kasa,inda shugaba mai ci Goodluck Jonathan ya sami nasara.