Babban jami’in harkokin diflomasiyyar Amurka a Afirka, Johnnie Carson, ya ce ya yi takaicin yadda tashin hankali ya dabaibaye zabukan da ake yi a Nijeriya kuma ya na kira ga hokumomin kasar su yi duk abinda su ke iyawa don tabbatar da cewa zabukan gwamnoni sun gudana cikin adalci da kwanciyar hankali a fadin kasar.
A rahoto na musamman da Mariama Diallo ta rubuta, t ace an fara ne da zaben ‘yan Majalisar Dokokin kasar, sai na Shugaban kasa kuma yanzu za a gudanar da zaben gwamnoni a yawancin jihohi 36 na kasar. Johnnie Carson ya ce, “Hakika ba a kammala ba har sai an gudanar da dukkannin zabukan uku.”
Mariama Diallo ta cigaba da cewa Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mai kula da Sha’anin Afirka Johnnie Carson ya dawo daga Nijeriya kwanan nan bayan ya shaidi yadda aka yi zaben ‘yan Majalisa a farkon wannan watan. Ya ce wannan zaben na karshe ya ma fi zabukan da su ka gabata muhimmanci.
Johnnie Carson ya cigaba da cewa, “Za mu sa ido kan wadannan zabukan sosai fiye ma da yadda mu ka yi game da zabukan das u ka gabata. Idan mu ka ga wani gwamna ko babban jami’in zaben da ke yinkurin magudi ko kuma tayar da fitina, za mu dau mataki kamar yadda mu ka yi a baya game da mutanen da su ka nemi gurgunta dimokaradiyya a wasu sassan Afirka.”
Mariama ta cigaba da cewa, “Nasarar da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi a makon jiya a kan Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa ta yi sanadin tashin hankali a sashin arewacin kasar. Masu sa ido na kasa da kasa sun ce da alamar an kamanta gaskiya a zaben. To amman Buhari, wanda tsohon shugaban Nijeriya ne na mulkin soji, na kalubalantar sakamakon zaben a kotu. An ce tashin hankalin da ya biyo bayan zaben ya yi sanadin mutuwar mutane 500.
Nijeriya ce kasar da ta fi samar da mai a Afirka kuma ta fi yawan mutane a inda ta ked a mutane 150.