Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomi A Nijeriya Na Ta Tabbatar Wa Masu Kada Kuri'a Cewa Babu Barazana Ga Rayuwarsu


A zabukan baya an baza 'yan sanda sosai don tabbatar da matakan tsaro lokacin zabe
A zabukan baya an baza 'yan sanda sosai don tabbatar da matakan tsaro lokacin zabe

Hukumomi a Nijeriya na ta tabbatar wa jama’a cewa babu wani hadari wajen fitowa kada kuri’a a zabukan gwamnonin jihohi, duk ko da mummunan tashin hankalin day a biyo bayan zaben shugaban kasa.

Hukumomi a Nijeriya na ta tabbatar wa jama’a cewa babu wani hadari wajen fitowa kada kuri’a a zabukan gwamnonin jihohi, duk ko da mummunan tashin hankalin day a biyo bayan zaben shugaban kasa.

Za a gudanar da zabukan ne a akasarin jihohi 36 na Nijeriya. To amman an jinkirta zabe a jihohin Kaduna da Bauchi na arewacin Nijeriya da kwanaki biyu saboda dalilai na tsaro.

Wata kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta ce tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar makon jiya ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 500.

‘Yan sanda sun ce an hallaka mutane uku sannan wasu 14 kuma su ka sami raunuka a tashe-tashen bama-baman birnin Maiduguri na arewa maso gabashin kasar. Hukumomi dai na zargin wata kungiyar Islama mai tsattsauran ra’ayi mai suna Boko Haram da kai harin.

‘Yan sanda na kuma zargin kungiyar ta Boko Haram da tayar da wani bam a birnin Maiduguri a jiya Litini wanda ya raunata wani dan sanda. Wani dan jaridan da ke wurin ya gaya wa Sashen Hausa na Muryar Amurka da alamar an auna wani wurin duba ababen hawa ne na ‘yan sanda da bam din to amman sai ya zarce ya fada cikin kwata, wanda hakan ya rage masa tasiri.

‘Yan sanda dai na ganin ‘yan gwagwarmayar Boko Haram na so ne su tsorata masu kada kuri’a tun kafin a fara zaben na yau Talata. Ma’anar lakabin wannan kungiyar dai ita ce tsarin ilimi na yammacin duniya haramun ne.

XS
SM
MD
LG