Wannan yana zuwa ne lokacin da hukumar ‘yan sandan kasar ta yaye jami'an da zasu rika taimakawa ‘yan sandan ga tsaron yankunan su.
Ga alama dai tura ta fara kaiwa bango ga tunzura jama'a da ‘yan bindiga ke yi, domin sun fara daukar matakan kare kansu daga ayyukan masu satar mutane har ma da hallaka su wani lokaci.
Abin da ke tabbatar da hakan shine wani atisaye da ‘yan sakai suka gudanar a garin Girkau ta karamar hukumar Kebbe a jihar Sakkwato, domin kare yankin su daga barazanar ‘yan bindiga.
Shugaban kungiyar ‘yan sakai na garin Girkau Abdullahi Chali a lokacin atisaye da suka yi domin shedawa ‘yan bindiga cewa sun shirya yin gaba da gaba da su, ya nunawa ‘yan jarida irin bindigar da zasu yi aiki dasu
Yahaya Na-Allah shima dan kungiyar ne na sakai, ya ce sun shirya bayar da rayukan su domin kare jama'ar su. Ya ce sace wasu mutanen su biyu da aka yi suka biya miliyan guda kudin fansa amma har yanzu ba a sako su ba da ma wasu batutuwan tsaro suka zaburar dasu daukar wannan mataki.
A dayan bangare kuma rundunar ‘yan sanda ta kammala bayar da horo ga jami'ai dari bakwai da hudu daga jihohin Sakkwato da Kebbi wadanda zasu taimakawa ‘yan sanda wajen kula da tsaron yankunan su.
Babban sufeton ‘yan sanda Muhammad Abubakar Adamu ta bakin mataimakin sa mai kula da yanki na Goma dake da ofishi a Sakkwato Muhammad Mustapha, ya ce jami'an wadanda sune rukuni na biyu da aka horas ana sa ran su bayar da gudunmuwa wajen samar tsaro a yankunan su.
Bisa la'akari da wadannan shirye shirye da ke gudana a halin yanzu ana iya cewa mai yiwuwa sha'anin tsaro ya inganta, musamman a yankunan arewa wadanda sune matsalar rashin tsaron ta dabaibaye.
Daga Sakkwato Muhammad Nasir ya aiko da wannan rahoto:
Your browser doesn’t support HTML5