Hakan ya biyo bayan gano wasu mutane 20 dake amfani da su suna damfarar wadanda basu ji basu gani ba, lamarin da masana tsaron yanar gizo da wasu ‘yan Najeriya suka yi marhaban da shi ganin bata suna da hakan ke yiwa kasar.
Kamfanin Meta dai ya kaddamar da wani gagarumin yaki a kan masu damfara ta yanar gizo wadanda aka fi sani da ‘Yahoo Boys a turance inda ya dauki matakin goge dubban asusun wasu ‘yan Najeriya da ke damfarar masu amfani da dandalin kudaddensu, lamarin da aka shafe tsawon shekaru ana kai ruwa rana a kai don kawo karshen shi.
Kamfanin ya goge shafuka dubu 2500 ciki da na wasu gungun mutane dake hadaka wajen yin damfara a sunan soyayya ta yanar gizo kamar yadda wani rahoton binciken kamfanin Meta mai taken, ‘Yaki da zamba da sunan so daga Najeriya.’
Wani 'dan Najeriya da aka taba damfara a shafin Facebook, Kabiru Aliyu Abubakar, ya yi marhaban da matakin da kamfanin Meta ya dauka yana mai cewa ba karamin taimakawa jama’a aka yi ba da wannan matakin.
A wani bangare kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum kuma ma’abocin mu’amala da dandalin Facebook da Instagram, Abubakar Muhammad Abujega ya ce matakin da kamfanin Meta ya dauka ya zo daidai da gaba kuma yana da mahimmancin ganin yadda ake ci gaba da batawa Najeriya suna ana korar masu zuba jari.
Matsalar masu damfara ta yanar gizo wadanda aka fi sani da Yahoo boys wanda ya samo asali daga hanyar sabis-sabis na imel, abu ne da ya shahara a Najeriya a tun daga shekarar 2000 inda ake alakatan su da ‘yan 419, waɗanda a da suka saba yin alƙawarin taimakawa baƙi su sami aiki ko arziki ta hanyar wasiƙu da imel daga baya a nemi kuɗi ya rikide zuwa ga damfara.
Masana tattalin arziki dai sun ce matsalar ‘yan damfara a yanar gizo na daya daga cikin tabargaza na baya-bayan nan dake tarnaki ga saka hannun jari a Najeriya, baya ga kawo sabani tsakanin ‘yan Najeriya da wadanda suka saba huldar kasuwanci da su suna janyewa lamarin da aka sha yin kira ga gwamnati ta dauki tsauraran matakai a kai don wanke Najeriya daga irin wannan laifuka a idon duniya.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5