'Yan Najeriya Na Iya Ci Gaba Da Zama A Afirka Ta Kudu - Jakada

Bayan da manzo na musamman daga shugaban kasar Afrika Ta Kudu ya gana da shugaban Najeriya, jakadan Najeriya a Afrika Ta Kudu, Kabiru Bala ya ce 'yan Najeriya na iya ci gaba da zama a kasar.

Biyo bayan hare haren kin jinin baki da wasu matasan Afirka ta Kudu suka kai kan ‘yan kasashen waje shugaba, Cyril Ramaphosa, ya turo da manzon na musamman zuwa Najeriya domin ba da hakuri kan abin da ya faru.

Mr. Jet Badare wanda ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock da ke Abuja, ya nuna alhinin gwamnati da al'umar Afirka ta Kudun kan aika-aikar da matasan kasarsa su ka yi.

Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudun ya shaidawa ‘yan jaridu a Abuja cewa, lalle gwamnatin Afirka ta Kudun na daukar matakan ganin an shawo kan matsalar don haka al'amura ka iya komawa daidai.

Jakada Kabiru Bala ya ce bisa la'akkari da irin wannan mataki da ake dauka a halin yanzu, ‘yan Najeriya da tuni suka fara tattara nasu ya nasu suna komowa gida, yanzu za su iya ci gaba da zama a kasar Afirka ta Kudun duba da wasunsu sun shafe shekaru 25r zuwa 30 suna zaune a kasar, wasu ma sun auri ‘yan kasar sun hayayyafa.

Jakadan ya kara da cewa, da dama daga cikin wasu ‘yan kasar masu kishin zaman lafiya ba sa jin dadin abubuwan da ke faruwa, al'amarin da ya sa wasu har zanga-zanga suka yi don nuna bacin ransu.

Masanin tsaro, Dr. Kabiru Adamu, ya ce ko da yake a matsayin jakadan Najeriya kuma jami'in diflomasiyya abin da ake tsammani ya fada kenan, amma gaskiya batun tabbatar da tsaron baki a Afirka ta kudu abu ne da ka iya daukar lokaci.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya Na Iya Ci Gaba Da Zama A Afrika Ta Kudu - Jakada