Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Tunawa Da Ranar Demokradiyya Ta Duniya A Jamhuriyar Niger


Bikin Tunawa Da Ranar Demokradiyya Ta Duniya A Jamhuriyar Niger
Bikin Tunawa Da Ranar Demokradiyya Ta Duniya A Jamhuriyar Niger

Yayin da aka yi hidimonin zagayowar Ranar Demokaradiyya Ta Duniya, wasu kwararru a janhuriyar Nijar sun tabo manufar tsarin na demokaradiyya, da kuma yadda wasu 'yan kalilan ke babakere a maimakon tafiya da kowa.

Yayinda aka yi bukukuwan tunawa da ranar demokradiya ta duniya a jiya Lahdi 15 ga watan satumba, masu rajin kare hakkin jama’a a Jamhuriyar Nijer sun bayyana damuwa game da yadda ake fuskantar koma baya wajen mutunta ka’idodin demokradiya a kasashe da dama a nahiyar Afrika, sakamakon jahilci da talakkawa ke fama da shi akan maganar ‘yanci.

Ganin yadda shuwagabanni ke fatali da ka’idodin demokradiya a kasashe masu tasowa, hakan ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 15 ga watan Satumba, domin tunatarwa akan mahimmancin wannan salon mulki, dake bukatar kiyaye hakkokin jama’a. Sai dai har yanzu wannan matsala na ci gaba da kamari a wasu kasashen Afrika a cewar Sanoussi Mahaman na kungiyar MPCR.

Demokradiya wani salon mulki ne da ake yi wa fassarar da mulkin al’umma, daga al’umma, domin al’umma, sai dai rashin sanin hakan ya sa, a yau talaka ba ya cin amfanin wannan matsayi da doka ta tanada dominsa inji Diori Ibrahim, daya daga cikin masu lakca a taron mahawarar da aka shirya, albarkacin wannan rana, wacce a bana aka maida hankali akan bukatar shigar kowane dan kasa a dama da shi.

‘Yan siyasa na kan gaba a sahun wadanda ake zargi da hannu wajen tabarbarewar demokaradiyya a kasashe masu tasowa, irinsu Nijer.

Alhaji Ibrahim Yakuba wani jagoran ‘yan adawa, ya ce, Matsalar tsaron da ake fuskanta a kasashen yankin sahel inda kungiyoyin ta’addanci suka addabi jama’a wata hanya ce da aka gano cewa gwamnatoci na amfani da ita don tauye hakkin ‘yan kasa, misalin yadda dokar ta baci ke takaita kai da kawon jama’a a yayinda take kara wa jami’an tsaro karfin iko.

Ga cikakken rahoton Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG