SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokutan da Gwamnatocin ke ta shagulglan cikar kwana 100 a kan karagar mulki, duk da yake ba abin da ya sauya a fannin samar da tsaron a wasu yankuna.
Matsalar rashin tsaro a iya cewa ita ce kan gaba ga dukkan matsalolin da suka dabaibaye al'ummomi musamman a Arewacin Najeriya.
Da yawa daga cikin masu rike da madafun iko sun alkarwanta magance matsalar ta tsaro a lokacin yakin neman zabe.
Bayan da suka soma mulki zuwa yanzu sama da kwana dari, mazauna wasu yankunan Arewa sun ce har yanzu babu abin da ya sauya.
Jihar Kebbi da ke Arewa maso yammacin kasar na daga cikin yankunan da matsalar ke addabar mutane musamman a kudancin jihar,.
Wasu daga cikin mazauna jihar sun ce har yanzu ba ta sauya zani ba.
A jihar Sokoto da ke makwabtaka da jihar ta Kebbi, mutanen da ke zaune a gabashin jihar su ne suka fi shan ukubar matsalar 'yan bindiga.
Su ma sun ce ba su ga tasirin alkawuran da 'yan siyasa suka yi musu na samar da tsaro ba.
Sai dai a wasu yankuanan mazauna wuraren sun ce akwai sauki kadan kamar yadda wani mutumen Sabon Birni Lukman ya shaidawa Muryar Amurka.
Jama'a da dama na ganin gwamnatin Najeriya dai karkashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu, ta kasa magance wannan matsalar duk da alkawura da ta yi akan hakan a wadannan yankunan.
Sai dai Gwamnatin jihar Sakkwato ta ce ta samar da motoci ga jami'an tsaro domin taimakawa ga ayukkan su.
Abin jira a gani ko motocin za su yi tasiri wajen saukaka matsalar, wanda yake a baya ma gwamnatoci sun yi ta bai wa jami'an tsaro motoci domin samar da tsaro, kuma kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5