'Yan Najeriyar 2; Olutayo Sunday Ogunlaja mai shekaru 39 da Abel Adeyi Daramola mai shekaru 37 za su raba shekaru 40 na zaman gidan kaso a tsakaninsu saboda taka rawa a yaudarar soyayya.
Sanarwar da babban lauyan Amurka, Alexander Uballez da dan sandan ciki mai kula da ofishin hukumar FBI, mai yaki da manyan laifuffuka ta Amurka na lardin Albuquerque, Raul Bujanda sun bayyana ta ma'aikatar shari'a cewa an yankewa mutanen 2 hukunci ne biyo bayan shari'ar kwanaki 4 da kasa da sa'o'i 3 na tattaunawa.
Mutanen 2 sun aike da kimanin dala dubu 560 zuwa asusun ajiyar banki daban-daban a kasashen Amurka, Kanada da Malaysia a tsakanin watan Janairun 2016 da Afrilun 2017.
Sakamakon hukuncin da aka zartar, kotu ta bada umarnin Ogunlaja da Daramola su ci gaba da kasancewa a karkashin ka'idojin saki har sai an zartar musu hukunci, wanda har yanzu ba'a tsayar da lokaci ba.
Idan aka zartar da hukuncin, kowane daga cikin Ogunlaja da Daramola zai shafe shekaru 20 a gidan kaso ba tare da damar samun afuwa ba.