Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fursunoni 33 Sun Mutu Wasu 1,534 Sun Arce Sakamakon Fasa Kurkuku A Mozambique


Fuusunoni 1534 Sunka Arce Sakamakon Fasa Kurkuku A Mozambique
Fuusunoni 1534 Sunka Arce Sakamakon Fasa Kurkuku A Mozambique

Tarzomar da ta tashi a kurkukun Maputo, babban birnin Mozambique ta hallaka mutane 33 tare da jikkata wasu 15, kamar yadda babban kwamandan 'yan sandan kasar, Bernardino Rafeal ya bayyana a jiya Laraba

Kasancewar har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankulan dake da nasaba da zaben da ya gudana a watan Oktoban da ya gabata wanda ake takaddama a kansa.

Hukuncin da kotun kolin Mozambique ta yanke a Litinin din da ta gabata wanda ya tabbatar da nasarar jam'iyyar Frelimo da ta jima a kan mulki ya sabbaba zanga-zangar gama-gari a fadin kasar daga kungiyoyin 'yan adawa da magoya bayansu dake da'awar cewa an tafka magudi a zaben.

A yayin da Rafeal ke zargin zanga-zangar dake faruwa a wajen kurkukun da karfafa gwiwar tarzomar cikinsa, Ministar Shari'a Helena Kida ta shaidawa wata tashar talabijin mai zaman kanta, Miramar TV cewa a kurkukun tarzomar ta samo asali kuma ba ta da alaka da zanga-zangar dake faruwa a wajensa.

"Rikicin da ya biyo bayan tarzomar ya yi sanadiyar mutuwar mutane 33 tare da jikkata wasu 15 a harabar kurkukun," kamar yadda Rafeal ya bayyana a hirarsa da manema labarai.

Har yanzu ba a fayyace bayanan mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba.

Kimanin fursunoni 1, 534 sun arce daga kurkukun sakamakon tarzomar amma an yi nasarar sake kama 150 daga cikinsu, a cewar Rafael, inda ya kara da cewa fursunoni sun yi yunkurin arcewa daga wasu gidajen yarin 2.

Muna cikin damuwa a matsayinmu na kasa, kuma 'yan kasar Mozambique sannan jami'an tsaro," a cewar Rafael, " muna sa ran karuwar laifuffuka nan da sa'o'i 48."

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG