Ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne wasu mayakan kungiyar Boko Haram suka sace dalibai ‘yan mata 276, a makarantarsu da ke garin Chibok a jihar Borno.
‘Yan mata 57 sun gudo da kansu, sannan a watan Oktoba na shekarar 2016 gwamnatin Najeriya ta karbo ‘yan mata 21, sannan sojoji suka uku, wanda jimilla ta zama 81.
Duka dai ‘yan mata 107 ne gwamnati ta iya karbowa a cikin shekaru hudu.
Yanzu haka dai akwai sauran ‘yan mata 112 a hannun kungiyar Boko Haram.
Cikin shekara hudun ne aka samu wata kungiya da ake kira ‘Bring Back Our Girls’ da ke fafutukar ganin an kwato ‘yan matan, wanda yunkurin da kungiyar ta yi ne ya sa aka san labarin sace ‘yan matan a duk fadin duniya.
Kungiyar kullum tana yin zama a dandalin hadin kan kasa na Unity Fountain da ke Abuja.
Ana kuma cikin wannan hali ne aka sami labarin sake sace wasu dalibai na makarantar sakandare ta Dapchi da ke jihar Yobe, a halin yanzu an dawo da 104 saura yarinya guda mai suna Leah Sharibu.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5