Wasu 'yan mata uku daga Najeriya, Seun Adigun, Ngozi Onwumere, da Akuoma Omeoga, sun shiga jerin waddanda za su wakilci kasashen su a wasan motsa jiki na shekarar 2018, wanda za a yi a Pyeong Chang a babban birnin Koria daga 9 ga wata zuwa 25, ga watan Fabarairu.
‘Yan matan uku sun shiga tarihi na zama ‘yan wasan Afrika na farko, maza ko mata don samun damar shiga cikin wassanin motsa jiki da ake yi akan kankara, bayan kammala wassani biyar da ake bukatar su kammala.
Wadannan ‘yan mata sun samu tikitin zuwa wassanin motsa jiki kan kankara na shekarar 2018, a Pyeong Chan, dake Kudancin Koria bayan kamamla wasan su na hudu da na biyar a Calgary, a kasar Canada, ranar laraba. Seun Adigun wacce ita ce daya daga cikin ‘yan wasan zamiya kan Kankara na kasar Amurka a shekarar 2015, ta yi murna kwarai bisa nasarrar da ‘yan Najeriya suka samu ta shiga wassanin.