'Yan Majalisun Dokokin Amurka Na Nunawa Juna Yatsa

‘Yan Majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Democrat da Republican dake ci gaba da ganin laifin juna, yayin da aka kawo karshen ranar farko a halin da ya kai ga rufe wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka, sun cima jituwa akan wasu batutuwa kalilan amma suna ci gaba da takaddama kan samar da sauyi a dokokin shige da fice.

A jiya Asabar shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattijai Mitch McConnell, ya ce ya shirya sake gudanar da kada kuri’a ranar Litinin da karfe ‘daya na dare, kan sabon kasafin kudi da zai iya dawo da harkokin gwamnati har zuwa ranar 8 ga watan Fabarairu.

Kuri’ar da za a kada zata matsa lamba ga ‘yan Majalisun jam’iyyar Democrat kan su amince da yarjejeniya ko a fuskanci sake rufe ayyukan gwamnati a karo na biyu.

Kudaden gudanar da gwamnati sun kare tun karfe goma sha biyun ranar Asabar, wanda ya haddasa rufe wasu harkokin gwamnati marasa muhimmanci sosai.