An shiga yini na farko a halin da ya kai ga rufe ma’aikatun gwamnatin Amurka bayan da majalisar dattawan kasar ta gaza cimma matsaya kan kasafin kudi na wucin gadi.
Shi dai wannan kasafin kudi shi zai ba da dama a ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnatin har zuwa cikin watan Fabrairu.
Amma juya baya da ‘yan jam’iyar Democrat suka yi na kin amincewa da wannan kudirin kasafin kudi ya kai ga an wayi gari daga 12 daren jiya Juma’a, gwamnati ba ta da ko sisi aljihunta.
Bukatar 'yan Democrat ita ce a samar da sauyi a dokokiin shige da ficen Amurka, wanda suka ce zai kawo karshen shirin DACA.
DACA, wani shiri ne da ya ke kare wasu dubban baki mazauna Amurka da suka shiga kasar tun suna yara, shirin da Shugaba Trump ya ce zai rushe.
Yanzu haka, dubun dubatar ma'aikatan gwamnati ba za su fita aiki ba, yayin da ake kokarin neman maslaha a majlisar dokokin.
Yayin da ake wannan takaddama, ga kadan daga cikin fannonin da matakin zai shafa kamar yadda jaridun Amurka suka wallafa:
- Wuraren da ake gudanar da binciken a fannoni daban-daban ciki har da kimiyya.
- Wuraren yawon shakatawa za su iya kasancewa a rufe.
- Takardun da tsoffin sojojin kasar masu nakasa suka gabatar domin neman tallafi za su iya fuskantar jinkiri.
- Ayyukan maido wa da ‘yan kasa kudaden haraji zai fuskanci jinkiri
- Miliyoyin yara da ke samun tallafin kiwon lafiya daga gwamnati.
- Dakarun Amurka da ke bakin aiki, (mai yiwuwa, ba za a biya su ba amma za su fita.)
- Za a dakatar da sauraren kararraki da suka shafi kananan laifukan na shafi fararen hula.
Sai dai ba daukacin ma’aikatan gwamnati ba ne za su ki zuwa bakin aiki lura da muhimmacin wasunsu, ga kadan daga cikinsu kamar yadda jaridun kasar suka wallafa:
- Ma’aikatan kula da filin sauka da tashin jiragen sama.
- Ma’aikatan da ke kula da kan iyakokin Amurka.
- Ma’aikatan isar da wasiku.
- Ma’aikata masu shara (musamman a birnin Washington)
- ‘Yan majalisar dokokin Amurka. (ba kamar sauran ma'aikatan da za su je aiki ba biya ba, su za a biya su.)
- Za a ci gaba da sauraren kararraki kan manyan laifuka a kotu. (misali kwamitin Robert Mueller da ke binciken katsalandan din Rasha a zaben Amurka zai ci gaba da aiki.
Rufe ma’aikatun gwamnatin da aka yi na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2013 a lokacin zamanin mulkin Barack Obama.
Kwanaki 16 aka kwashe a wancan lokacin ma’aikatun na rufe.
Saurari fashin bakin Farfesa Yusuf Alhassan, Malami a jami’ar jihar Missour kan wannan hali da ake ciki a hirarsa da Mahmud Lalo, inda ya fara bayani kana abin da ke nufi da rufe ma’aikatun gwamnati:
Facebook Forum