'Yan Majalisar a kasar Somaliya sun baiwa hammata iska

Wakilan Majalisar wakilan kasar Somaliya, a cikin zauren Majalisar

Laraban nan fada ya gwabje tsakanin yan Majalisa a kasar Somaliya, kwana daya bayan da wasu yan Majalisa suka jefa kuri'ar tsige kakakin Majalisar Sharif Hassan Sheikh Adnan

Fada ya gwabje tsakanin yan Majalisar wakilan kasar Somaliya, kwana daya bayan da wasu yan Majalisa suka jefa kuri'ar tsige kakkakin Majalisar Sharif Hassan Sheikh Adnan.

An fara fada ne bayan da wakilai wadanda basu goyon bayan Adnan suka yi kokarin zaben wanda zai maye gurbinsa, wanda lokacinda suke kokarin nada shi baya kasar yana kasar Italiya. Magoya bayan kakkakin da aka tsige, sai suka yi ta kururuta rashin amincewarsu, nan da nan sai bangarorin biyu suka fara naushin juna.

Wani shedan gani da ido ya fadawa sashen Somaliya na Muryar Amirka cewa, har wasu yan Majalisar guda biyu sunji 'yan rauni.

Ita dai gwamnatin rikon kwarya Somaliya dama tana fuskantar matsaloli da suke sa kafar angulu ga yunkure yunkuren da ake yi na daidaita al'amurra a kasar.

Fafitukar baya bayan nan, a ranar Talata aka fara, lokacinda wakilai maitan da tamanin daga cikin wakilan Majalisar dari biyar da hamsin suka jefa kuri'ar tsige kakkakin Majalisar.

Yan Majalisar sunyi kukar cewa kakaki Adnan yaki wakilan Majalisar suyi muhawara akan muhimman batutuwa, ciki harda taswirar makomar harkokin siyasa kasa da tsara sabon tsarin mulkin kasar.

Su kuma magoya bayan kakakkin sunce, ba'a bin hanyoyin da suka dace na tsige kakkakin ba, a saboda haka har yanzu shine kakkakin Majalisar.

Aika Sharhinka