'Yan Libiya Sun Binne Kwamandan Askarawan Tawaye

  • Ibrahim Garba

'Yan tawayen Libiya kenan dauke da gawar babban Kwamandan askarawan 'yan tawayen

Dubban ‘yan Libya sun fito yau jumma’a a Benghazi babbar cibiyar

Dubban ‘yan Libya sun fito yau jumma’a a Benghazi babbar cibiyar ‘yan tawaye domin binne kwamandan sojojin adawar kasar.

An bindige aka kashe Abdul fattah Younis da wasu mataimakansa biyu jiya alhamis a wani yanayin da har yanzu ba a san zahirinsa ba. Kwamandan yana daya daga cikin manyan na hannun damar shugaba Muammar Gaddafi kafin ya koma bangaren ‘yan tawayen a farkon wannan shekara.

Jiya alhamis, shugaban gwamnatin wucin gadi ta ‘yan tawaye yace an kashe mutanen uku kafin su isa gaban wani kwamitin bincike na shari’a domin amsa wasu tambayoyi da suka shafi ayyukan soja.

Amma da farko, ‘yan tawayen sun ce an kama Younis bisa zargin cewa har yanzu iyalansa su na da alaka da gwamnatin shugaba Gaddafi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Mark Toner, ya fada yau jumma’a cewa mutuwar Younis babban kalubale ne ga ‘yan tawayen a saboda irin kwarewarsa a fagen daga da kuma shugabanci.