Ministan harakokin cikin gida na gwamnatin shugaban Libya Mua’ammar ghadacfi ya bayyana a a birnin Alkahira, babban birnin kasar Misra, tare da danginsa su 9, a wani abinda ake ganin kamar wata alama ce dake nuna shima ya gujewa gwamnatin ta Libya.
Jami’an kasar ta Masar sunce da sanyin safiyar yau Litinin ne ministan, Nassr al-Mabrouk AZbdullah da dangin nasa suka iso Alkahira a cikin wani jirgin chata da ya taso daga tsibirin Djerba na kasar Tunisia.
Sai dai jami’an sunce a bisa kan takardar izni ta viza irin wacce ake baiwa masu yawon bude ido ne ministan da iyalin nasa suka zo, kuma ba wani jam’in opishin jakadancin Libya dake nan Masar da ya tarbe su.
Wani rahoto ya ruwaito wata majiya daga Djerba na cewa mukarraban na Gaddafi sun yi ta tattaunawa da 'yan tawaye a wani otal din da aka samar da tsauraren matakan tsaro a ranar Lahadi.
A wani sakon da aka yada ta gidajen talabijin da safiyar yau Litini, Mr. Gddafi ya umurci mutane da su yi abin da ya kira gwagwarmayar kwato Libiya daga 'yan tawaye maciya amana, kamar yadda ya bayyana su.
'Yan tawayen dai na kan dannawa ga hedikwatarsa da ke birnin Trabulus. Jiya Lahadi sun yi ikirarin karbe iko da sassan muhimmin garin nan na Zawiyya, wanda ikirari ne da gwamnati Libiya ta yi watsi da shi.