A yau Talata ne babban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai dawo ya ci gaba da muhawara akan wani kuduri da ake neman a zartas na yin Allah-waddai akan gallazawar da gwamnatin Syria ke yi wa al’ummarta, musamman masu yi mata zanga-zangar nuna mata kyama. Yau ne ake shiga rana ta biyu da soma wannan muhawara akan matakin da shugaban Syria din, Bashar al-Assad yake dauka na tura ma’aikatansa na tsaro suna fattatakar dimbin mutanen dake tarukkan zanga-zangar nuna wa gwamnatinsa kyama. Mazauna garin Hama sunce a jiya ma tankunan sojan sun sake dawowa garin, kwana guda bayanda harbe-harben da sojoji suka yi a garin. kampanin dillacin labarum Reuters ya ruwaito wasu mazauna garin na cewa an kashe akalla mutane ukku a lokacin da sojan na gwamnati suka bude wuta akan garin na Hama. Duka-duka mutane kamar ishirin da hudu aka hallaka a irin wadanan hare-haren da soja suka kai a sassan kasar daban-daban jiya Litinin. A halin yanzu kuma, Syria ta fama da matsin-lambar kasashen duniya da dama dake kira akanta da ta daina wannan fatattakar da take wa al’ummarta, abinda ya janyo har kasar Italiya ta janye jakadanta dake kasar a yau. Ita ma Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, a yau take shirin ganawa da wasu ‘yan hankoron neman-chanji na Syria a nan Washington, yayinda Kungiyar tarayyar Turai ta dada saka takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma cafke kadarorin karin wasu mukrrabai biyar na gwamnatin Syria, ciki har da ministanta na tsaro, Ali Habib Mahmud.
Babban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai ci gaba da tattaunawa domin yin Allah wadai kan gallazawa bil'dama da gwamnatin kasar Syria ke yi
A yau Talata ne babban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai dawo ya ci gaba da muhawara akan wani kuduri da ake neman a zartas na yin Allah-waddai akan gallazawar da gwamnatin Syria ke yi wa al’ummarta, musamman masu yi mata zanga-zangar nuna mata kyama.