Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya bayyana amincewa da sojojinshi, duk da yunkurin kashe she da wadansu sojoji suka yi makonni biyu da suka shige. A cikin hirar da Muryar Amurka tayi dashi, Mr. Conde yace ana yiwa rundunar sojin garambawul, wadda a halin yanzu runduna ce ta “jamhuriya” karkashin ikon farin kaya. Shugaban kasar ya bayyana cewa, wadansu manyan jami’an sojoji basu ji dadin canje canjen ba, kuma bisa ga tunaninsu, inji shi, suna gani kamar mutuwa ta zata maida kasar Guinea mawuyacin halin da take ciki da. Sai dai, bisa ga cewar Mr. Conde ba zaka iya tauye ci gaban tarihi ba. Mr. Conde ya tsallake rijiya da baya a wadansu hare hare biyu da aka kaiwa gidanshi dake Conakry babban birnin kasar ranar 19 ga wannan wata na Yuli. Jami’an kasar Guinea sun ce sun kama mutane 38 makon jiya dangane da hare haren, 25 daga cikinsu jami’an sojoji. Tsohon hafsan hafsohi janar Nouhou Thiam na daya daga cikin mutanen da aka fara kamawa. An zabi Mr. Conde shugaban kasa watan Nuwamban bara a zaben da yafi sahihanci a tarihin kasar Guinea tun shekara ta dubu da dari tara da hamsin da takwas
Shugaban kasar Guinea ya bayyana amincewa da rundunar sojin kasar duk da yunkurin kashe shi da aka yi
Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya bayyana amincewa da sojojinshi, duk da yunkurin kashe she da wadansu sojoji suka yi makonni biyu da suka shige.