Masu zanga zangar maza da mata na ‘dauke da hotunan Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa Zeenatu da kuma ‘ya ‘yan Malamin da suka rasu a Zariya. A zanga zangar jiya da sukayi a Abuja sunci karo da ‘yan sanda da suka jefa musu barkonon tsohuwa.
Mai zaman mataimakin shugaban ‘yan Shi’a a Najeriya Mallam Yakubu Yahaya, ya kalubalanci abin da ya kira hana ‘yan Shi’ar yin Ibadarsu, da caccakar gwamnatin jihar Kaduna bisa matakin da ta dauka.
Malamai na kungiyoyin Ahlus Sunnah sun yaba da matakin da gwamnatin Kaduna da yadda jami’an ‘yan sanda a Abuja suka bukaci ‘yan Shi’an suke rika neman Izini kafin yin muzahara.
Shari’a kan batun ci gaba da tsare Mallam Ibrahim El-Zakzaky na gaban babbar kotun Najeriya, inda lauya Feme Falana ke kare bangaren ‘yan Shi’a.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5