Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Boko Haram Ta Sauya Salon Kai Hare-hare


Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram

Yayinda sojojin Najeriya ke cigaba da samun nasara akan yakin da su keyi da 'yan ta'adan kungiyar Boko Haram, ita ko kungiyar sake salon kai hare-hare tayi inda yanzu kauyukan da basu da dakarun taro take bi tana aiwatar da ta'addanci.

Yanzu 'yan ta'adan Boko Haram suna bin kauyuka ne suna kone gidaje tare da sace abinci , kuma wani zibin har da kashe mutane.

Harin baya bayan nan sun kai ne a karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa. Sun kai kan wasu kauyuka ne inda babu jami'an tsaro da suka kusa da kan iyaka da jihar Borno. A kauyukan sun kone gidaje tare da sace abinci. Wasu mazauna kauyukan sun tsera rijiya da baya.

Bayan 'yan ta'adan sun yi kone kone a kauyukan sojojin Najeriya sun isa wuraren sun fatattaki 'yan ta'adan.

Rundunar 'yansandan jihar Adamawa ta kakakinta Usman Abubakar ta tabbatar da wannan sabon harin na Boko Haram. A sanarwar da rundanar ta fitar ta gargadi jama'a su dinga sa ido tare da bada rahotan duk abun da basu yadda dashi ba. Yace a cikin mutanen garin akwai wasu da suke cikin kungiyar suna zaune a garin suna taimakawa 'ya abOko Haram da baynai. Yace suna sa idanu akan irin wadannan mutanen kuma zasu kamasu.

Yanzu a jihar Adamawa 'yan kato da gora ko maharba su ne suke kula da wasu garuruwan da aka kwato.

Sarauniyar maharban jihar Adamawa tace suna samun nasara akan 'yan ta'addan.

Ga rahoton Ibraim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG