Jamus na iya yin hakan ne ta bada taimako da kayan aiki da bada horo da kuma taimakawa da labarun siri ga mayakan ruwan kasar ta Najeriya..
Shugaban Najeriya yayi wannan furucin ne yayinda ya karbi bakuncin ministan harkokin wajen kasar Jamus Dr. Frank-Walters Steinmeier a fadarsa dake Abuja.
Shugaba Buhari yace "Ana sace man Najeriya ana bi dashi ta yankin Gulf ta Guinea. Horaswa da ba mayakan ruwanmu kayan aiki zasu dakile satar", inji Buhari.
Shugaba Buhari ya fadawa bakon nasa cewa an shawo kan kalubalen tsaro a arewa maso gabashin kasar yayinda aka kusa murkushe 'yan Boko Haram amma kuma wata matsalar tsaro ta kunno kai a yankin Niger Delta. Manufar ita ce a sake mamaye kasar, a durkusar da tattalin arzikinta ta lalata ma'aikatun man fetur da iskar gas. Muna tattaunawa da shugabanninsu mu san kungiyoyi nawa ne kuma muna aiki da kamfanonin mai dake yankin" inji Buhari.
Buhari yace mayakan sa kai din suna amfani da hanya mai sarkakiya tare da yin anfani da horon da suka samu walau daga kamfanonin mai ko gwamnati suna lalata bututun mai da gine gine da suke karkashin teku. Akwai bukatar mu san masu tada kayar bayar domin mu tattauna dasu domin su da mu mu samu karfin gwuiwa" inji Shugaba Buhari.
Da yake maida martani Jakadan Jamus Dr Steinmeier yace Jamus tana farin cikin jin kokarin da gwamnatin Buhari keyi na kawar da 'yan ta'ada a arewa maso gabashin kasar. Yace ashirye suke su taimakawa Najeriya domin shawo kan matsalar Niger Delta.
Jakadan ya yabawa Najeriya da yakin da ta keyi da cin hanci da rashawa. Dr. Steinmeier yace gwamnatin kasarsa na goyon bayan yakin dari bisa dari.. Ya kara da cewa Jamus nada sha'awar saka jari a Najeriya..
Yace Jamus zata goyi bayan cigaban kasa tare da cewa suna son dangataka ta kud da kud musamman a harkokin da suka shafi raya birane da ba sojojin ruwa kayan aiki da horo.