Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Shirin Fadakar da Mata Akan Sa Sarari Tsakanin Haihuwa


Likitan kiwon lafiya aNijar
Likitan kiwon lafiya aNijar

A cikin wani shirin fadakarwa da gwamnatin Nijar tayi ana cigaba da wayar da kawunan mata akan mahimmancin barin yaro ya yi kwari ya kai kamar shekaru biyu da haihuwa kafin a yi wani cikin, wato a sa sarari tsakani.

Matar shugaban kasar Nijar wadda ita ma likita ce tare da ministan kiwon lafiya suka kaddamar da shirin na tsawon mako daya a birnin Dosso.

Makasudin fadakarwar shi ne rage mace macen da da uwa domin haihuwan yara a jere babu wani lokaci da yakamata tsakaninsu yana yiwa iyaye da yaran da ake dora masu kanne tun basu gama rarrafe ba nada la'ani.

Malam Hassan Haruna jami'in asibitin sadarwar dake birnin Kwanni yayi karin bayani akan makon. Yace a kasashe masu tasowa talakawa na yawan mutuwa lokacin haihuwa. Wannan fadakarwar tana cikin kokarin da gwamnati keyi na taimakawa mata da zummar rage mace mace.

Yawan haihuwa akai akai kan kashe mahaifa saboda ba'a bata lokacin warkewa ba kafin wani cikin ya shigo. A cikin wannan yanayi yaron da aka hana shan nono sosai domin sabon ciki ya shigo shi akan rasa. Ana gargadin mata su yaye 'ya'yansu tukunna kafin su dauki wani cikin.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG